8 Disamba 2017 - 17:15
An sace Shugaban PDP na Filato

Wasu da ba Asan ko su wanene ba sun sace shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Filato Hon Damishi Sango tare da iyalan sa akan hanyar su ta zuwa Abuja domin halartar taron Jam’iyyar na kasa.

Yan sandan sun ce sun kaddamar da bincike yanzu haka akan mutanen da ba a tantance ba.

Wannan dai na zuwa ne a yayin da jam’iyyar PDP ke kokarin gudanar da taron ta na kasa.
 Sakataren yada labaran Jam’iyyar John Akans ya tabbatar da aukuwar lamarin ,inda ya bayyana alhinin sa tareda bukatar ganin yan Sanda sun gudanar da aikin bincike mai zurfi